Papa Roma ya soki masu 'kyale-kyale' a Kirismeti

papa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Papa Roma Benedict

A lokacin addu'o'in kiresmeti na duk shekara a dandalin St Peters' dake birnin Roma, Papa Roma Benedict ya soki yadda ake maida Kirismeti tamkar wani abun kasuwanci.

Papa Roman ya kuma yi kira ga mabiya addinin kirista a duk fadin duniya su daina bin abubuwa na kawa ko kuma kyal-kyal banza.

Sannan kuma ya bukaci kiristoci su kasance masu yaada bishara ta asali.

Papa Roma mai shekaru 84 yayi amfani da wata na'ura mai tafiya don sakowwa zuwa tsakiyar dandalin.

'Mahaifar Yesu'

Dubun dubbatan masu ibadar Kirista ne da 'yan yawun bude ido suka yi tururuwa zuwa yamma da kogin jordan a garin Bethlehem, inda nan ne aka haifi Annabi Isa Alaihi Salam wato Yesu Kiristi, don fara bukukuwar Kirismeti tun a ranar Asabar.

An kiyasta taron na bana a matsayin wanda yafi kowanne a cikin fiye da shekaru goma.

An kamalla bukukuwan ne a cikin dare tare da addu'o'i a cocin Nativity, wanda aka ginashi a daidai wajen da ake ganin nan aka haifi Yesu Kiristi.

Shugaban kiristoci a birinin Kudus Fuad Twal yayi kira a samu zaman lafiya da tsaro a gabas ta tsakiya baki daya.

Karin bayani