An kashe jagoran 'yan tawaye a Darfur

ibrahim Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin Sudan sun ce sun kashe Khalil Ibrahim jagoran 'yan tawaye

Dakarun soji a kasar Sudan sun ce sun kashe shugaban kungiyar 'yan tawaye mafi girma a yankin Darfur wato Khalil Ibrahim na Justice and Equality Movement.

Kakakin sojojin Sudan, Sawarmi Khaled Sa'd ya shaidawa sashin larabci na BBC cewar an kashe Khalil Ibrahim ne gabda asubahi a garin Wad Banda dake arewacin jihar Kordofan.

Kawo yanzu dai babu wata majiya mai zaman kanta da zata iya tabbatar da wannan rahoton.

Shi dai Khalil Ibrahim ya dawo ne daga gudun hijira daga kasar Libya bayan faduwar mulkin Kanar Gaddafi wanda ke bashi taimakon kudi dana soji.

Jagoran 'yan tawayen ya kuma sanya hannu a yarjejeniyar tsagaita bude wuta da gwamnatin Sudan a watan Fabarairun bara amma daga bisani sai ya watsar da batun tattaunawa akan zaman lafiya.

Karin bayani