An kashe jagoran JEM a Kordufan

Taswirar Sudan Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Taswirar Sudan

Gwamnatin kasar Sudan ta ce ana ci gaba da gwabza fada a wani yanki dake kusa da arewacin Darfur, inda dakarun gwamnati suka kashe wani babban jagoran 'yan tawaye, Khalil Ibrahim da mayakansa su talatin.

A wata sanarwa, wani kakakin 'yan tawayen kungiyar Justice and Equality wato JEM, ya tabbatar da kisan shugaban nasu a wani harin da aka kai ta sama ranar juma'a.

Yanzu haka ministan yada labarai na gwamnatin Sudan din, Abdullah Ali Massar ya ce ana ci gaba ya yaki a kusa da kan iyakar tsakanin arewacin Darfur da jahar Kordofan.

Karin bayani