A Najeriya an yi addu'o'i ga wadanda suka rasu a harin Bam

bom Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mutane akalla arba'in sun mutu a harin ranar Kirismeti

Daruruwan Mutane ne suka halarci wata addu'a a Cocin Roman Katolikan da aka kashe mutane fiye da 30 a wani harin bam a jiya a Najeriya.

Harin bam din a wajen babban birnin kasar, Abuja, shi ne na farko a jerin hare haren a ranar Kirsimeti a kan Coci coci da gine ginen yansanda inda mutane fiye da 40 suka mutu.

Kungiyar masu Kishin Islaman nan ta Boko Haram ta ce ita ce ta kai hare haren.

Babban jagoran yan adawa na Najeriyar, Muhammadu Buhari ya zargi gwamnati da yin tafiyar hawainiya wajen mayar da martani game da lamarin.

An yi matukar Allah wadai da hare haren bama baman da aka kai ranar Kirsimati a Najeriya wadanda suka kashe mutane kusan 40.

Fafaroma Benedict ya bayyana goyon bayansa ga wadanda lamarin ya rutsa da su sannan ya bayyana hare haren da cewar wani mummunan aiki ne.

Karin bayani