'Yan Koriya ta Kudu na ganawa da sabon shugaban Koriya ta Arewa

koriya Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fitattun da zasu je Koriya ta Arewa don ta'aziyar mutuwar Kim Jung-Il

An bayar da rahoton cewar wasu fitattun maziyarta na Koriya ta Kudu sun gana da mutumin da aka zaba a matsayin shugaban Koriya ta Arewa na gaba, Kim Jong-Un.

Jami'an Koriya ta Kudu sunce Uwargidan tsohon Shugaban Kasar Koriya ta Kudu da kuma wata Shugabar wani babban Kamfani sun yi tattaunawa tare da Shugaban har ta tsawon kusan mintuna 10 bayan isarsu Pyongyang don jama'izar mahaifinsa Kim Jong-Il.

A cikin wata sanarwa Kakakinta Matar tsohon Shugaban Koriya ta Kudun, Yoon Chul-Koo - Lee Hee -Ho, ya ce ta yi fatan ziyarar za ta kyautata dangantaka tsakanin Koriya ta Kudu da ta Arewan.

Wannan dai shi ne taro na farko da aka sani tsakanin karamin Kim din da Yan Koriya ta Kudu.

Karin bayani