Fitattun mata biyu daga Koriya ta Kudu za su je Arewa

koriya Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fitattun da zasu je Koriya ta Arewa don ta'aziyar mutuwar Kim Jung-Il

Wasu fitattun 'yan Koriya ta Kudu biyu sun tsallaka kan iyaka zuwa Koriya ta Arewa don hadewa da 'yan kasar wajen juyayin mutuwar tsohon shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong -il.

Fitattun sune Lee Hee-Ho matar tsohon shugaban Koriya ta Kudu Kim Dae-jung, da kuma Hyun Jeong-eun wato shugabar kamfanin Hyundai.

Mazajen matan biyu dai sun taba ganawa ido da ido da margayi tsohon shugaban Koriya ta Arewa a kokarin ganin inganta dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Wakiliyar BBC tace "suna ziyarar ce don kashin kansu in ji hukumomi, kuma babu wani dan Koriya ta Kudu da za a barshi yaje ta'aziya zuwa Arewa duk da cewar Pyongyang ta bada takardar gayyata a bude.

Karin bayani