Ana sa ran isar tawagar kasashen larabawa yau a Syria

Masu zanga zanga a Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga zanga a Syria

Ana samun rahotannin karin tashin hankali a Birnin Homs na Syria.

Masu fafutikar kare hakkin Bil Adama sunce mutane har kusan 18 ne aka kashe a can a rana ta 3 ta mummunan ruwan harsasai.

Mace macen sun faru ne yayinda ake sa ran tawagar masu sa ido ta mutane kusan 50 na kungiyar kasashen larabawa, a Syriar domin sa ido a kan wata yarjejeniyar da suka amince kanta tare da Gwamnatin Syriar dda ke da aniyar kawo karshen tashin hankalin watanni 9.

Daga karshe dai tawagar za ta kasance da wakilai har dari biyu.

Wani Wakilin BBC a Lebanon mai makwabtaka ya ce, ba a dai sani ko ya Allah hukumomin Syria za su bayar da hadin kai ga tawagar ba.

To amma wani kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Syria, Jihad Makdissi ya shedawa BBC cewar 'yan kallon na kungiyar kasashen Larabawa, za su kasance da yancin zuwa ko'ina suke so.

Janar Muhammad Al Dabi ya ce tawagar za ta tattauna da kungiyoyi daban daban a Syria hadda 'yan adawa.

An kiyasta cewar akalla mutane dari biyar ne suka mutu a zanga zangar nuna kin jinin gwamnati.

Kungiyar 'yan adawa ta Syrian National Council ta yi kira ga tawagar ta fara zuwa birnin Homs inda ta ce a yankin Baba Amr akwai sojojin gwamnati fiye da dubu hudu masu azabtar da jama'a.

Karin bayani