Anna Hazare na yajin cin abinci

Anna Hazare Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Anna Hazare

Fitaccen mutumen nan dake fafutukar kare hakkin Dan Adam a India, Anna Hazare ya fara wani yajin cin abinci na kwanaki 3 a birnin Mumbai, yana neman gwamnati da ta zartas da dokar yaki da cin hanci da rashawa mai tsanani, fiye da wadda ake muhawara a kai yanzu haka a majalisar dokokin kasar.

Magoya bayan Mr Hazare din mai shekaru 74 da haifuwa, sun roke shi da ya kawo karshen yajin cin abincin nasa saboda damuwar da suke nunawa dangane da koshin lafiyarsa.

A cikin watan Agustan da ya gabata, wani yajin cin abincin da Mr Hazaren ya yi, ya samu goyon bayan dimbin jamaa, kuma ya tilastawa gwamnatin kasar ta India bullo da wani sabon daftarin dokar yaki da matsalar cin hanci, wadda ta yiwa kasar katutu.

Karin bayani