Dubban jama'a na zanga-zanga a Isra'ila

Masu zanga-zanga a Beit Shemesh Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu zanga-zanga a Beit Shemesh

Dubban 'yan Isra'ila suna gudanar da wata zanga-zanga don nuna adawa da halayyar Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi, wadanda ke son a aiwatar da tsarin ware maza da mata.

Shugaban Isra'ila Shimon Peres ya ce Yahudawa marasa rinjaye a Isra'ila suna keta dokokin dake karfafa hadin kan 'yan Isra'ila saboda haka ne ma ya karfafa wa jama'a gwiwa don su halarci zanga-zangar da ake yi a garin Beit Shemesh, kusa da birnin Kudis.

Garin na Beit Shemesh dai ya janyo fushin 'yan Kasar ta Isra'ila, tun bayan da wata yarinya mai shekaru 8 ta ce tana fargabar zuwa makaranta, sakamakon wani abun ban takaici da ya faru da ita, inda wasu maza Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi suka tofa yawu a kanta, suna masu zarginta da rashin sanya sutura madaidaiciya.

Karin bayani