Japan ta dage haramci sayarwa kasashe makamai

noda Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Pirayi Ministan Japan Yoshihiko Noda

Gwamnatin kasar Japan ta dage haramcin data sanya kanta akan fitar da makamai zuwa kasashen waje.

Sakataren gwamnatin kasar, Osamu Fujimura ya ce matakin zai taimakawa kasar ta hada hannu wajen kera wasu karin makaman ga wasu kasashen duniya tare da samarda kayayakin sojojin don ayyukan jin kai.

Mista Fujimura ya ce Japan zata sa ido matuka akan yadda zata dunga fitar da makamai zuwa kasashen waje saboda kaucewa rura wutan rikici.

A halin yanzu dai Japan ta haramtawa kanta sayarda makamai a kasashen ketare saidai kawai ga Amurka.

Karin bayani