Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 1500 a Phillipines

philipines
Image caption Ambaliyar ruwa a Phillipines

Akalla mutane dubu daya da dari biyar ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwan da aka yi na fiye da mako guda a kasar Phillipines.

Hukumomi sun ce an kara gano wasu gawawwakin a saman ruwa kusada tsabirin Mindanao. Kawo yanzu dai ba a iya gane yawan mutanen da suka bace ba, amma dai hukumomi sun ce za a cigaba binciken gawarwakin.

Hukumar agajin gaggawa a kasar ta ce za a shafe watanni shida kafin a kamalla gina gidaje na wucin gadi ga mutane dubu sittin din da suka rasa matsugunansu.

Masu hasashen yanayi sun kara gargadin cewar za a iya samun wani ambaliyar ruwa a nan gaba.

Richard Gordon shugaban kungiyar agaji ta Red Cross a Phillipines ya shaidawa BBC cewar "matsin lambar da ake ciki a yanzu shine a ranar 3 ga watan Junairu dole ne wadanda suka rasa gidajensu su bar makarantu, a don haka zamu kawo tantuna ne a cikin gari, abinda muke kokarin shiryawa kenan".

Karin bayani