An kasa gano bakin zaren zaman lafiya a Jos

jos
Image caption Har yanzu ana zaman dar dar a Jos

Yanzu dai kimanin shekaru goma kenan ana fama da tashe-tashen hankula masu nasaba da kabilanci da addini da kuma siyasa a jihar Filaton Nijeriya inda dubban mutane suka rasa rayukansu baya ga hasarar dimbin dukiya, amma kawo yanzu lamarin ya ki ci ya ki cinyewa. Rigingimun na jihar Filato sun dade suna janyo hankalin kungiyoyi da hukumomi na cikin gida a Najeriya da kuma na kasashen duniya.

A yanzu haka ma kotun duniya mai hukunta manyan laifukan yaki wato ICC wacce ke da Shedikwata a birnin Hague na gudanar da bincike domin duba yiwuwar gurfanar da manyan mutane da ake zargin su na da hannu a yawan zubadda jinin. Ana dai zargin hukumomi a jihar ta Filato da ma Najeriyar baki daya da gazawa wajen shawo kan matsalar.

Karin bayani