Putin ya soki 'yan adawa

Vladimir Putin Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Vladimir Putin

Piraministan Rasha, Vladimir Putin, wanda zai sake tsayawa takarar zaben shugaban kasa a cikin watan Maris mai zuwa, ya bayyana 'yan adawan kasar da cewa ba su da wani buri, kuma ba su da shugabanni na kwarai.

Wannan da si hi ne karon farko da Mr Putin din ke yin irin wadannan kalamai, tun bayan macin da 'yan adawan kasar ta Rasha suka yi a birnin Mosko a ranar Asabar da ta gabata.

A wani jawabi da yayi wa 'ya'yan jam'iyyarsa ta All Russia People's Front, Mr Putin ya yi kakkausar suuka ga abun da ya kira yunkurin da wasu ke yi na nuna rashin halalcin sakamakon zaben 'yan majalisar dokokin da aka yi a farkon wannan watan.

'Yan takarar da dama ne dai suka yanke hukuncin kalubalantar Mr Putin din a zaben da ke tafe, amma shi ne ake ganin zai yi galaba.

Karin bayani