Tawagar kasashen Larabawa tana Homs na Syria

Wani gini na ci da wuta a birnin Homs Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wani gini na ci da wuta a birnin Homs

Wata tawagar 'yan kallo na kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ta isa birnin Homs na Syria don tabbatar ko gwamnatin kasar tana mutunta 'yarjejeniyar da aka kulla da nufin kawo karshen murkushe masu zanga-zanga da gwamnatin ke yi.

Masu fautika sun ce gwamnati ta janye wasu daga cikin tankokin yaki daga birnin , gabannin isar tawagar.

Sai dai wakilin BBC ya ce shugaban tawagar ya ce kawo yanzu gwamnatin Syriar tana ba su hadin kai.

Birnin na Homs dai yana daya daga cikin cibiyoyin da ake gudanar da zanga-zangar nuna kyamar gwamnatin Syriar.

A can ne aka yi tashin hankali mafi muni a cikin 'yan watannin da suka wuce, yayinda rahotanni suka ce an kashe akalla mutane 30 a birnin a jiya Litinin.

Masu fafutika sun ce dubban jamaa suna zanga-zanga a birnin domin nuna adawa da gwamnati.

Karin bayani