Amurka ta gargadi Iran kan mashigin ruwa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption shugaba Obama na Amurka

Amurka ta ce ba zata sake lamuntar duk wani cikas da kasar Iran zata kawo ba, kan harkokin sufurin jiragen ruwan kasashen duniya ta mashigin ruwan Hormuz, hanyar da kashi daya cikin uku na tankokin daukar mai na duniya ke amfani da ita.

Furucin Amurkar ya biyo bayan barazanar da mataimakin shugaban kasar Iran ya yi ne a jiya, cewa zasu rufe mashigin ruwar na Hormuz, idan har kasashen yammacin duniya suka kuskura suka sa takunkumin hana sayen man kasar ta Iran.

Wani wakilin BBC a Washington ya ce martanin da Amurkar ta mayar kan furucin na Iran, an yi shi ne cikin taka tsantsan, amma kuma ba tare da boye boye ba.

A kodayaushe ana ci gaba da yi ma juna kallon hadarin kaji ne, tsakanin Iran da Amurka da kuma sauran kasashen yammacin duniya, game da shirin nukilliyar Iran.

Iran na cewa shirin nukiliyar ba na kera makamai ba ne, yayinda kasashen yamma ke cewa makamin nukiliya take kokarin kerawa.

Labaran BBC