Mutane 15 sun rasa rayukansu a Burma

Wuta a Burma Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wani abu mai karfin gaske da ya fashe a Burma ya janyo asarar rayuka

Akalla mutane goma sha biyar ne suka halaka bayan fashewar wani abu mai karfin gaske a Burma

Wasu da dama kuma sun jikkata.

Fashewar abin dai ya auku ne cikin dare a harabar wani gidan ajjiye kayayyaki dake gabacin birnin Rangoon kuma lamarin ya janyo wuta ta cinye yankin.

Ba a dai san menene abinda ya janyo fashewar abin ba. Wadanda suka ganewa idanunusu sunce uku daga cikin mutanen da suka mutu masunta ne.

An dai ce gidan ajjiye kayayyakin na dauke ne da sinadarai da kuma kayayyakin aikin gini da kuma na samar da gishiri

Wakilin BBC yace mazauna kusa da yankin sun ce sun ji wata kara mai karfi, sannan kuma sun ga hayaki yana tashi sama

Karin bayani