An bayyana Kim Jong Un a matsayin shugaba

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Taron jama'a a Pyongyong, Koriya ta Arewa

An bayyana dan autan marigayi Kim Jong-il a matsayin sabon jagoran Korea ta Korea a wani biki da dimbin jama'a suka halarta a birnin Pyongyang.

Kim Jong-un ya jagoranci addu'o'in da aka yi wa mahaifinsa, inda manyan shugabannin soja da na jam'iyya suka rufa ma sa baya.

An yi ta jawabai na yabon marigayin a gaban dubun dubatar sojoji da fararen hula, wadanda suka yi cincirido, sun sunkuyar da kawunansu, a babban dandalin birnin na Pyongyang.

Yanzu dai Kim Jong -un, shi ne sabon shugaban kasar ta Korea ta Arewa da rundunar sojin kasar da kuma jam'iyyar dake mulkin kasar.

An bayyana shi da cewa mutum ne mai akida da halayya irin ta mahaifinsa.

Ko a jiya shi ya jagoranci jana'izar da aka yi wa mahaifin nasa, inda aka ratsa da akwatin gawarsa ta titunan birnin Pyongyang, inda ja'ama suka yi ta rusa kuka.

Karin bayani