Shugabannin majami'u a Najeriya sun gargadi gwamnati

Jami'an tsaro a Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugabannin majami'u a Najeriya sun gargadi gwamnati

Shugabannin majami'u a Najeriya sun ce mambobinsu za su kare kansu idan har jami'an tsaron Kasar suka gaza wajen kare lafiyar su.

Shugaban Kungiyar mabiya addinin Kirsita a NajeriyaPastor Ayo Oritsejafor yace ba zai bukaci Kiristocin su yi ramuwar gayya ba, amma ya ce zai neme su da su kare kawunansu .

Shugaban Kiristocin ya kuma nemi gano su wanene ke daukar nauyin masu kai hare-hare a Najeriya

Ana dai cigaba da zaman dar-dar tun bayan wasu jerin hare-hare da Kungiyar nan ta Boko Haram tace ita ta kai a wasu majami'u a cikin Kasar, harin da ya yi sanadiyar mutuwar kusan mutane arba'in.

Mutane dubu casa'in ne kuma suka tsere daga gidajensu sakamakon tashe- tashen hankula a garin Damaturu dake arewa maso gabacin kasar.

Karin bayani