Turkiyya ta kashe mutane 35 a wani hari

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gawarwakin mutanen da aka kashe a hare haren Turkiyya.

Mahukunta a kasar Turkiyya sun ce an kashe mutane talatin da biyar a wasu jerin hare hare da kasar ta kai ta sama a arewacin Iraqi.

Mahukuntan sun ce an nufi kai harin ne kan Kurdawa masu tada kayar baya, sai dai kuma wasu majiyoyin Kurdawan sun ce wadanda aka kashen, masu fasa kwauri ne da aka yi zaton mayakan kungiyar 'yan aware ne ta PKK.

Majiyoyin sun ce wadanda aka kashe din na dauke ne da iskar gas ne da sukari dake suke kokarin shigarwa cikin yankin kudu maso gabashin Turkiyyan.

Gidan talabijin na Turkiyyar ya nuna hotunan jerin gawarwakin mutanen, lullube da barguna a gefen wani tsauni.

Karin bayani