Ba zamu canza manufar mu ba - Koriya ta Arewa

Manyan jami'an gwamnatin Koriya ta Arewa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Koriya ta Arewa ta ce manufofinta ba su canza ba

Koriya ta Arewa tace babu abinda zai canza dangane da manufofinta duk kuwa da canjin shugabancin da aka samu a Kasar.

A sanarwar kasar ta farko, tun bayan da aka bayyana Kim Jong- Un a matsayin sabon Shugaban Koriya ta Arewan, Hukumar tsaron Kasar tace Koriya ta Arewan ba zata cigaba da kulla wata alaka ba tare da Koriya ta Kudu .

Sanarwar Koriya ta Arewan ta kara da cewa kada shashashan 'yan siyasa a duniya suyi tsammanin wani abu zai canza yanzu.

Wakilin BBC yace jami'an diplomaciya na Kasahen Amurka da China da Koriya ta Kudu da Japan zasu ziyarci junansu, domin tattauna tasirin canjin shugabancin Koriya ta Arewan da kuma matakin da zasu dauka a nan gaba

Karin bayani