Kokarin daidaita al'ammura a Sudan ta Kudu

Wani makiyayi a Sudan ta Kudu

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Wani makiyayi a Sudan ta Kudu

Majalisar Dinkin Duniya ta tura wata rundunar zaratan sojoji zuwa garin Pibor dake Sudan ta Kudu domin hana barkewar rikici tsakanin kabilu biyu da ke gaba da juna.

Kimanin 'yan bindiga dubu shida ne daga kabilar Lo Nuwar ke yin kutse cikin jahar Jonglei suna kona gidaje suna kuma kwace shanun 'yan kabilar Murle.

Wakilin BBC ya ce a 'yan sa'o'in da suka wuce dubban 'yan kabilar Murle sun tsere daga garin Pibor suna fargabar kawo musu hari.

Shugaban ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Sudan ta Kudu, Lise Grande ya shaidawa BBC cewa MDD ta tura sojoji zuwa Pibor domin su taimaka wa dakarun sojin Sudan ta Kudun.