Neman sasanta kabilun Nuer da Murle a Sudan

Sudan ta Kudu
Bayanan hoto,

Sudan ta Kudu

Majalisar Dinkin Duniya ta tura wata rundunar zaratan soji zuwa wani gari a Sudan ta Kudu domin hana barkewar rikici tsakanin kabilu biyu da ke gaba da juna.

Amma kuma mahukunta a wajen sun shaidawa BBC cewa duk da wannan karin da akai, sojojin baza su isa ba.

Gwamnan janar Jonglei ya ce mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudun, Riek Marchar na kokarin shiga tsakanin kabilun Lo Nuwer din da na Murle.

Inda ya ce Dr. Riek Marchan na garin Pibor yana kokarin maganawa da mayakan Lo Nuwer, yana kiran da su koma gida.

Kimanin 'yan bindiga dubu shida ne daga kabilar Lo Nuwar ke dannawa garin Pibor, abinda yasa dubban 'yan kabilar Murle ke ta tserewa daga garin.