Masu zanga-zanga a Syria na shirin fitowa yau

Masu zanga_zanga a Syria Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Za a gudanar da zanga- zanga a Syria yau juma'a

Masu fafutuka 'yan adawa a Syria sun yi kira ga mutane dasu fito kan tituna a yau juma'a, ranar da aka saba warewa domin gudanar da zanga zanga.

A yanzu haka dai wata tawaggar Kasashen labawa tana Syrian domin sa ido akan yarjejeniyar zaman lafiya.

Masu aiko da rahotanni sunce masu fafutuka na fatan jama'a zasu fito sosai, kuma hakan zai nunawa tawaggar Kasasahen larabawan yadda mutane suka fusata.

Masu fafutuka a Syrian dai sun zargi dakarun gwamnatin Kasar da kashe mutane da yawansu ya kai har arba'in a jiya alhamis.

Wakilin BBC yace tura masu sa ido na kassahen larabawa cikin kasar ga alamu ma ya kara tunzura al'amura ne kawai

Karin bayani