An yi sabuwar zanga-zanga a Yemen

Masu zanga-zanga a Yemen Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu zanga-zanga a Yemen

Dubban jama'a sun sake gudanar da zanga zanga a duk fadin Yemen inda suke ci gaba da neman da a gurfanar da shugaba Saleh a gaban shari'a.

Zanga-zangar na zuwa ne yayin da ake ci gaba da rade-radin cewa Mr Saleh, wanda ya yi murabus bayan kwashe watanni ana zanga zanga, mai yuwa nan bada jimawa ba ya bar kasar, watakila ya wuce Amurka.

Masu zanga zangar dake maci suna rera taken manufarsu na cewa tilas ne su kasance tsintiya madaurinki daya, domin cimma burinsu na juyin-juya hala.

Suna kuma nuna damuwa kan cewa na hannun daman Mr Saleh, ciki har da 'ya'yansa, za su ci gaba da kasancewa kan mulki, duk da yarjejeniyar da aka cimma kan mika mulkin a watan da ya gabata.

Karin bayani