Sojojin Ethiopia sun kama wani gari a Somalia

Wani sojan al Shabaab Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wani sojan al Shabaab

Sojojin Ethiopia sun kwace wani muhimmin gari a Somalia daga hannun 'yan kungiyar masu fafutika ta al Shabaab inda suka yi amfani da motoci masu sulke da makaman igwa wajen kai hari a kan garin na Beledweyne.

Kakakin gwamnatin Ethiopia, Bereket Simon, ya ce gwamnatin rikon kwariyar Somalia ta TFG ce ta yi kira ga kasashe makwabta da suka hada da Ethiopia da su taimaka ma ta da sojoji, saboda haka ne suka yi katsalandan a Somaliar.

Kungiyar ta Al Shabaab dai ta ce dakarunta sun yiwa garin kawanya, bayan da suka shirya janyewa da kansu, a matsayin wata dabarar yaki. Garin na Beled-weyne dai yana da muhimmancin sosai ta fuskar tsaro, kuma yana kusa da iyaka da Ethiopia kan babbar hanyar dake kaiwa birnin Mogadishu.

Karin bayani