'Yan kallo na kasashen Larabawa sun nuna damuwa a Syria

Masu zanga-zanga a Syria Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu zanga-zanga a Syria

Rahotanni sun ce masu sa ido na kungiyar kasashen Larabawa dake ziyara a Syria, sun bayyana damuwa game da yadda gwamnatin kasar ta girke sojoji masu boyewa suna harbin mutane daga rufin gine-gine.

Kamfanin dillancin labaran Jamus, DPA ya ruwaito, wata majiya ta kusa da tawagar, tana cewa tawagar jami'an na kasashen Larabawa sun yi kira ga gwamnatin Syria da ta janye sojojin daga rufin gine-ginen nan take.

Wani faifan video da aka saka a Intanat, ya nuna daya daga cikin jami'an tawagar a birnin Deraa, yana fadawa masu zanga-zanga cewa ya ga sojojin dake buya suna harbin mutane, da idanunsa.

Wakilin BBC ya ce baa iya tantancen sahihancin videon ba, amma ga alama ya nuna jami'in yana cewa idan baa janye sojojin a cikin sa'o'i 24 ba, to kungiyar kasashen Larabawa za ta dauki mataki.

Karin bayani