Korea ta Arewa ta nemi sadaukarwar yan kasar ga jagoransu

Kim Jong Un Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption shugaban kasar Korea ta Arewa Kim Jong Un

Korea ta Arewa ta fitar da sakon ta na sabuwar shekara, inda ta umurci yan kasar da su kare sabon shugabansu Kim Jong-Un, da rayuwarsu.

Sakon ya bayyana cewa, jamiyya mai mulki, da rundunar sojin kasar da daukacin alummar Korea ta Arewa, su shirya idan bukatar hakan ta taso, don kare shugaban su da rayuwar, ko da ran su zai tafi.

Wani sharhi da jaridar kasar ta yi, na nuna cewa, Korea ta Arewa na fuskantar matsalar karancin abinci, inda ta yi kira da a dauki matakan shawo kan matsalar.

Shi dai Kim Jong-un ya zamanto jagoran Korea ta Arewa ne makonni biyu da suka gabata, bayan rasuwar mahaifinsa Kim Jong-il.