Dokar ta baci ta kankama a Maiduguri

Sakamakon harin da aka kai da bam a Maiduguri Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sakamakon harin da aka kai da bam a Maiduguri

Dakaru dauke da makamai da tankokin yaki ne ke yin sintiri a Maiduguri babban birnin Jihar Borno.

Hakan dai ya biyo bayan da Shugaba Jonathan ya ayyana dokar ta baci a wasu sassan arewacin kasar da matsalar hare haren yan kungiyar Boko Haram ta addaba.

Shugaba Goodluck Jonathan dai ya saka dokar ta bacin ne a sashen arewa maso gabacin kasar da birnin Jos mai yawan fama da rikice rikice da kuma wani sashe na Jihar Neja dake kusa da Abuja babban birnin kasar a jiya.

An rufe kan iyakoki da Kamaru da Chadi da kuma Nijar.

Kusan mako guda kenan dai da Kungiyar masu kishin Islaman ta Boko Haram ta kai hari a wasu sassa na kasar a ranar Kirsimeti, hade da a kan wani Coci , inda aka kashe mutane akalla 37 sannan aka jikkata wasu 57.

Karin bayani