Iran ba za ta kawo cikas ga zurga zurgar Jiragen ruwa a Hormuz ba

Wani makami mai linzami da Iran ta gwada Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani makami mai linzami da Iran ta gwada

Iran ta ce ba za ta kawo cikas ga zurga zurgar jiragen ruwa a Mashigin ruwa na Hormuz ba, abinda ke nuni da sassauci a kan barazanar da ta yi a cikin makon da ya wuce game da hanyar ruwan mai cike da hada hada.

Mashigin ruwan dai na daya daga cikin manyan hanyoyin dakon mai, kuma Iran ta ce za ta iya datse shi idan kasashen yammacin duniya suka saka takunkumi a kan fitar da manta.

Wakilin BBC a Tehran ya ce kasar ba za ta iya toshe mafitar da man kanta ba.

Wakilin na BBC ya ce Iran na samun rabin kudin shigarta ne daga danyen man da take fitarwa,kuma matsanancin tsadar mai shi ke rike Gwamnatin Iran duka da kudi da kuma iko.

Iran ta bayar da sanarwa ne a ranar karshe ta atisayen sojin ruwanta a mashigin ruwa na Hormuz, inda ta samu nasarar kara gwada wasu makaman masu linzami biyu.

Karin bayani