Rikici ya lafa a garin Pibor na Sudan ta Kudu

Yan gudun hijira a Sudan ta Kudu
Bayanan hoto,

Yan gudun hijira a Sudan ta Kudu

Rahotanni daga Sudan ta Kudu, na nuna cewa yan kabilar Lou Nuer da suka kai kimanin dubu shidda, sun janye daga garin Pibor.

Sun mamaye mamaye garin ne na wani lokaci, don daukar fansa kan harin da yan kabilar Murle suka kai masu.

An kona wasu gine gine, sannan akwai rahotannin cewa mutane da dama sun jikkata.

Dubun dubatan yan kabilar Murle ne suka yi kaura daga garin Pibor, wadda ke karkashin kulawar dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu.