Dubban mutane sun tsere wa wani rikicin kabilanci a Sudan ta Kudu

Shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu

Majalisar dinkin duniya na gargadin kauyukan Sudan ta Kudu da su tsere da rayukansu gabanin isar mayakan da ke karatowa na wata kabilar da ba sa ga maciji da juna.

Dubban yan kabilar Murle ne aka raba da gidajensu sakamakon wani hari da yan kabilar Lou Nuer suka kai.

An kwace wasu sassan garin Pibor, sannan aka cunna wa wani asubiti wuta.

Majalisar dinikin duniyar dai tana da bataliya guda a garin; wanda kuma wani ayarin sojin Sudan ta Kudu ke rike da shi.

Gwamnati dai za ta aikewa da karin yansanda da dakaru.

Karin bayani