Kungiyar Taliban zata bube Ofis a Qatar

'Yan kungiyar Taliban Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan kungiyar Taliban

Yan Kungiyar Taliban a Afghanistan sun ce sun cimma wata 'yarjejeniya da za ta share fagen bude wani Ofis da zai kula da harkokin siyasa na kungiyar a kasar Qatar.

Masu sharhi kan al'ammura dai suna daukan batun bude Ofis din na 'yan Taliban a matsayin wani mataki mai muhimmancin gaske wajen farfado da tattaunawar zaman lafiya tsakanin gwamnati da masu tada kayar baya a kasar ta Afghanistan.

Wakilin BBC yace sanarwar ta kungiyar Taliban ta tabatar da radi radin da ake akan cewa masu tada kayar baya me yuwa su bude ofishin siyasa a kasar Qatar.

Karin bayani