Mitt Romney da Rick Santorum sun yi kankankan

'yan takarar kujerar shugaban Amurka karkashin inuwar jam'iyar Republican Mitt Romney da Rick Santorum sune ke kan gaba a zaben fidda da gwani na Jam'iyar da aka gudanar a jihar Iowa.

Bayan kidaya kusan daukacin kuri'un da aka kada a jihar, kowanne cikin 'yan takarar guda biyu ya samu kashi ashirin da biyar-biyar na kuri'un da aka kada, inda suka tserewa abokin karawarsu Ron Paul.

Wannan dai shine zaben fidda gwani na farko da magoya bayan Jam'iyyar suka gudanar don tsayar da dan takarar da zai kalubalanci Barrack Obama a zaben shugaban kasar da za'a gudanar a watan Nuwamba.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan takarar shugaban Amurka karkashin inuwar jam'iyar Republican

Rahotanni sun ce jihar ta Iowa nada matukar muhimmanci saboda duk dan takarar da yayi nasara, zai samu karin magoya baya a Amurkan tare da samun karin kudaden gudanar da yakin neman zabe, inda kuma akan tilastawa wadanda basu tabuka wani abin azo a gani ba a zaben fidda gwanin, janyewa daga takarar.