Amurka ta yi watsi da gargadin Iran

Hakkin mallakar hoto Getty

Amurka tace zata cigaba da turawa da jiragen ruwa dake dauke da jiragen saman yaki zuwa yankin Gulf duk da gagardin da Iran tayi akan ta daina yin haka.

Ma'aikatar tsaro ta kasar ta ce Amurka zata cigaba da tura sojojinta na ruwa kamar yadda ta saba yi a shekaru da dama da suka gabata.

Da farko rundunar sojin kasar Iran tayi barazanar daukar mataki idan wani jirgin ruwan Amurka me dauke da jiragen saman yaki da ya bar yankin na Gulf ya sake komawa wurin.

Karin bayani