Tattaunawar Gabas ta Tsakiya za ta farfado

shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas Hakkin mallakar hoto AP
Image caption shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas

Masu shiga-tsakani daga bangarorin Isra'ila da Falasdinawa za su gana a karo na farko cikin fiye da shekara guda, a wani yunkuri na farfado da tattaunawar sulhu a Gabas ta Tsakiya.

Za su gana ne a Jordan, don binciko hanyoyin da za su sake komawa kan teburin shawarwarin zaman lafiya na kai-tsaye.

Wakilin BBC ya ce Isra'ila da Falasdinawa suna taka-tsantsan wurin bayyana fatansu kafin taron, wanda wakilan Majalisar Dinkin Duniya da na Amurka da Rasha da Tarayyar Turai za su halarta.

Tattaunawar sulhun dai ta lalace ne a shekarar 2010, bayan da Isra'ila ta ci gaba da gina matsugunan Yahudawa 'yan kama wuri zauna a Yammacin Kogin Jordan, yankin da suka mamaye.

Karin bayani

Labaran BBC