Kotu ta hana 'yan kwadago yajin aiki a Najeriya

Hakkin mallakar hoto facebook

Kotun warware rikicin ma'aikata da gwamnati a Najeriya ta umurci kungiyoyin kwadagon kasar da kada su fara yajin aikin da suka shirya shiga a ranar Litinin mai zuwa.

Wannan hukuncin dai ya baiwa hukumomin kasar damar tarwatsa duk wata zanga zanga dake da alaka da batun janye tallafin man fetur a kasar.

Sai dai a wata sanarwa da ta fitar, kungiyar kwadago ta Najeriya NLC, ta ce ba gudu ba ja da baya a yajin aikin da ta shirya yi a ranar Litinin mai zuwa.

Kungiyar kwadagon ta kuma yi kira ga 'yan Najeriya da su yi watsi da hukuncin da ta kira na wasan yara.

A kwankin bayane gwmanatin Najeriya ta ce zata janye tallafin da take baiwa bangaren man fetur a kasar, abunda ya sa kudin kayan masarufi da sufuri ya yi sama.

Zanga-Zanga

Jama'a a sassa dabam-daban na kasar na ci gaba da nuna adawa da matakin gwamnatin kasar na janye tallafin man fetur din.

A Abuja babban birnin kasar, wasu daruruwan matasa sun gudanar da zanga-zanga don nuna rashin amincewarsu da matakin.

Daga cikin wadanda suka yi wa matasan jawabi sun hada da tsohon ministan Abuja, Malam Nasiru el-Rufa'i da, Cif Femi Fani Kayode, tsohon ministan sufuri, da Hon. Dino Melaye, tsohon dan majalisar wakilai.

Haka nan an gudanar da makamanciyar zanga-zangar a jihohin Sakkwato, da Kaduna da Niger da kuma birnin Warri a jihar Delta.

A waje daya kuma wani taro da shugabanin hukumomin tsaro suka gudanar a hedkwatar 'yan sanda dake Abuja, ya bukaci a gudanar zanga zangar cikin tsanaki, ba tare da tayar da hankali ba.

Sifeto Janar din Najeriya Hafiz Ringim, ya ce 'yan Najeriya na da 'yancin gudanar da zanga-zanga da yajin aiki cikin lumana domin neman gwamnati ta sauya wata manufa, kuma 'yan sanda za su bada kariya ga lafiya da dukiyoyin al'umma matukar aka gudanar da yajin aikin.

An yi wata ganawa tsakanin Shugaba Jonathan da gwamnonin kasar a ranar Juma'a, sai dai babu wata sanarwa kan hakan.

A ranar Litinin ne kungiyar kwadago ta kasa ta nemi a gudanar da zanga zangar gama-gari da yajin aiki, domin adawa da janye tallafin.

Karin bayani