Ana ci gaba da zanga-zanga a Najeriya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

A ci gaba da nuna damuwa bisa cire tallafin mai a Najeriya, a yau wasu kungiyoyi na matasa, da na kare hakkin bil adama da na dalibai sun gudanar da zanga zanga a jihohi da dama na kasar.

Matasa sunyi zanga zanga a Kaduna, da Bauchi, da Gombe da Katsina.

A jihar Kano, matasa na cigaba da zaman durshen da suke yi. Ita ma a nata bangaren, kungiyar lauyoyi ta kasa reshen jihar Lagos, ta gudanar da wata zanga zanga a birnin Lagos, domin nuna adawa da janye tallafin kan man petur.

Shugabannin lauyoyin sun ce farashin man fetur da a yanzu ake sayar da kowacce lita daya akan naira 141 , ya haifar da tsadar kayan masarufi.

Masu zanga zangar dai na kira ne ga gwamnati data maida tallafin man.

Sai dai a nata bangaren, gwamnatin ta ce ba makawa sai an janye tallafin

Karin bayani