N'Dour na neman shugabancin kasar Senegal

Youssou N'dour
Image caption Youssou N'dour

Sanannen mawakin nan na kasar Senegal kuma mai fafutukar siyasa, Youssou N'dour, ya bayar da sanarwa cewa zai tsaya takarar shugabancin kasar a zaben watan Fabrairu.

Mawakin ya ce yana amsa kiraye-kirayen mutane ne don ya kalubalanci shugaban kasar mai ci, Abdoulaye Wade, wanda ke takara a karo na uku.

Youssou N'dour ya dade yana shiga harkar kare hakkin jama'a, inda ya kasance wakili ga asusun tallafawa yara na Majalisar Dinkin Duniya.

Wakilin BBC ya ce ba karamin aiki ne ga Youssou N'dour ya ja ra'ayin dubban masoya wakokinsa su zabe shi ba.

Karin bayani

Labaran BBC