Michele Bachmann ta janye daga takarar fidda gwani a Amurka

Hakkin mallakar hoto GETTY IMAGES

'Yar majalisar wakilan Amurka daga jihar Minnesota, Michele Bachmann, ta janye daga takarar zaben fidda gwani na jam'iyyar Republican domin zaben shugaban kasar da zaa yi a bana.

Mrs Bachmann, wadda Kirista ce mai ra'ayin rikau, ta samu kashi 5 ne kacal daga cikin 100 na kuru'un da aka kada a zaben fidda gwanin da aka yi jiya a jihar Iowa.

Tsohon gwamnan jihar Massachusetts ne, Mitt Romney ya samu nasara a zaben na Iowa da dan karamin rijaye inda ya kada Rick Santorum da kuru'u 8 kacal daga cikin kuru'u dubu dari da 20 da magioya bayan jam'iyyar suka kada. .

Karin bayani