Mitt Romney ya yi nasara a zaben farko

Mitt Romney Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mitt Romney

Tsohon gwamnan jihar Massachusetts, Mitt Romney ya yi nasara da dan kankanin rinjaye a zaben farko na fidda gwani na jam'iyyar Republican na Amurka, don fidda dan takarar da zai tsayawa jam'iyyar takara a zaben shugaban kasa.

Mr Romney ya kada abokin takararsa, Rick Santorum, wanda wani tsohon Sanata ne, da rinjayen kuri'u takwas daga cikin kuri'u dubu dari da ashirin da aka kada a jihar Iowa.