Ina da karfin gwuiwa kan Burma: in ji Hague

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mr Hague da shugaban kasar Bama

Sakataren harkokin wajen Birtaniya William Hague ya ce yayi imanin sabuwar gwamnatin farar hula ta kasar Burma da gaske take wajen aiwatar da sauye sauye.

Mr Hague ya bayyana haka ne a ranar farko ta ziyarar da yake a Burma, ziyarar da ita ce ta farko da wani sakataren harkokin wajen Birtaniya ya kai kasar, cikin sama da shekaru hamsin.

Bayan tataunawar da aka sha yi da jami'an gwamnati har mada shugaban kasar Burma Thein Sein, Mr Hague cewa yayi ya samu karfin gwiwa a bisa abinda kunnuwansa suka ji.

Amma yace daukacin duniya zasu yanke hukunci kan wanan gwamnati gwargwadon yanayin abubuwan data aikata.

Ya kuma ce akwai bukatar kara kokarin ganin cewar an sako fursunonin kasar.

Jagorar masu fafutukar kafa Demokradiyya a Burma, Aung San Suu Kyi, ta ce sauye-sauyen siyasar da ake yi a kasar , na tafiyar hawainiya, amma ta ce tana sa ran a gudanar da zabubuka bisa tafarkin Demokradiyya a lokacin da take raye.