An ci gaba da zanga zanga kan cire tallafi a Nijeriya

Wasu masu zanga zanga a  Nijeriya. Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wasu masu zanga zanga a Nijeriya.

A Najeriya, jama'a na ci gaba da nuna adawa da matakin gwamnatin kasar na janye tallafin man fetur, lamarin da tuni ya sa farashin kayan masarufi ya yi sama.

A Abuja babban birnin kasar, wasu daruruwan matasa sun gudanar da zanga zanga don nuna rashin amincewarsu da matakin da gwamnatin kasar ta dauka na janye tallafin man fetur.

Daga cikin wadanda suka yi wa matasan jawabi sun hada da tsohon ministan Abuja, Malam Nasiru el-Rufa'i da, Cif Femi Fani Kayode, tsohon ministan sufuri, da Hon. Dino Melaya, tsohon dan majalisar wakilai.

Haka nan an gudanar da makamanciyar zanga zangar a jihohin Sakkwato, da Kaduna da Niger da kuma birnin Warri a jihar Delta.

A waje daya kuma wani taro da shugabanin hukumomin tsaro suka gudanar a hedkwatar 'yan sanda dake Abuja, ya bukaci a gudanar zanga zangar cikin tsanaki, ba tare da tayar da hankali ba.

A yau an yi wata ganawa tsakanin Shugaba Jonathan da gwamnonin kasar, sai dai babu wata sanarwa kan hakan.

A ranar Litinin ne kungiyar kwadago ta kasa ta nemi a gudanar da zanga zangar gama-gari da yajin aiki, domin adawa da janye tallafin.

Karin bayani