Mutane da dama sun hallaka a Syria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Harin bam da wani dan kurnar bakin wake ya kai a Syria

Gidan talibijin na Syria ya ce wani harin kunar bakin wake a Damascus babban Birnin kasar ya hallaka mutane dadama.

Ya ce 'yan tadadda ne suka kai harin a unguwar Midan, wadda mattatar masu adawa ta gwamnati ce.

Sai dai masu fafutuka, sun zargi gwamnatin kasar da shirya harin wanda ya kuma jikkata mutane dadama.

Fashewar abin ya faru ne a tsakiyar unguwar Midan dake babban birnin Damascus.

Gidan talabijin na kasar ya nuna hutunan titunan da abin ya yi faru faca-faca da jini.

Gidan talabijin din dai yace mutane da dama sun mutu kuma wasu sun sami raunuka. Inda ya kara da cewa wani dan kunar bakin wake ne ya kai harin.

Akwai rahotannin dake nuna cewa an kai harin ne kan wata mota kirar bus ta jami'an 'yan sanda, kuma baya ga 'yan sanda akwai fararen hula ma na cikin wadanda suka mutu.

Harin dai ya zo ne mako biyu bayna fiye da mutane arba'in sun mutu a wasu tawayen hare-haren da aka kai a tsakiyar birnin na Damascus.

Gwamnatin Syria dai ta dora alhakin kai harin kan kungiyar AlQa'ida.

Sai dai kungiyoyin 'yan adawa na zargin gwamnatin da kai harin don jan hankalin masu sa ido na kungiyar kasashen larabawa dake kasar don sa ido akan tashin hanklain dake faruwa.