An kama tsohon babban hafsan sojin Turkiya

Image caption Janarar Basbug

Hukumomin Turkiyya sun tsare tsohon babban hafsan rundunar sojin kasar, Janar Leker Basbug, sun kuma tuhumeshi da jagorantar wata kungiyar 'yan taadda.

Wani abu kuma da ake zargin janar din dashi, shine cewa ya yi yunkurin hambaradda zababbiyar gwamnatin Firaministan kasar Tayyip Erdowan.

Janaral Basbug wanda ya yi murabus daga mukaminsa na jagorancin rundunar sojin Turkiyya mai fada a ji a shekarar da ta gabata, ya jima yana sukar gwamnatin Pira Minista tayyip Erdowan mai sassaucin ra'ayin Islama.

Duk da haka, kame shi da tsare shi ya baiwa mutane da dama mamaki. An yi masa tambayoyi har na tsawon sa'oi bakwai kafin a kulle shi.

Janaral Basbug dai ya musanta zarge-zargen.

Zargin ya biyo bayan binciken da aka shafe shekaru uku ana yi a kan wani yunkuri na wasu masu tsatsauran ra'ayin kishin kasa na kifar da gwamnati.

Kamen Janar bash boo na zuwa ne awanni bayan ya bada shaida a shari'ar da ake yi wa wasu 'yan jarida da ake zargi da gudanar da wani shafin intanet da ke goyon bayan kungiyar da ake zargi da yunkurin kifar da gwamnatin, wacce kuma ake zargin sojoji da mara musu baya.