Gwamnatin Birtaniya ta yi gargadi game da hare haren ta'addanci a Kenya

William Hague, Sakataren Harkokin wajen Birtaniya Hakkin mallakar hoto PA
Image caption William Hague, Sakataren Harkokin wajen Birtaniya

Gwamnatin Birtaniya ta fitar da sanarwa dake gargadin masu ziyara a Kenya cewa akwai alamu masu karfi dake nuna yuwuwar kai hare haren ta'addanci.

Wakiliiayr BBC ta ce, sanarwar na cewa an yi imanin cewa bisa dukkan alamu wasu 'yan ta'adda na matakan karshe na kai wasu hare hare.

Sanarwar ta ce don haka ya kamata masu kai ziyara su guji kusantar wasu gine gine na gwamnati, da ma sauran wurare da baki masu ziyara suka saba taruwa, kamar otel otel , da kasuwanin da gabar teku.

Jami'an Birtaniya na sashen yaki da ayyukan ta'addanci na na taimakawa 'yan sandan Kenyar, wadanda suka gano wasu nakiyoyi da kayan hada bamabamai a wani samame da suka kai a Mombasa cikin watan jiya.

Karin bayani