Ana kai hare-hare a kan 'yan kudancin Najeriya

'Yan sandan Najeriya

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

'Yan sanda a Najeriya sun ce an kashe akalla mutane 14 a Mubi, Jihar Adamawa

’Yan sanda a Najeriya sun ce ’yan bindiga sun kashe akalla mutane goma sha hudu a wani hari da aka kai kan wani dakin taro da ke garin Mubi a Jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin kasar ranar Juma’a.

Rahotanni sun ce wasu ’yan bindigar kuma wadanda ba a san ko su wanene ba sun kai hari a Yola, babban birnin jihar ta Adamawa, a daren ranar Juma’ar.

Wadansu rahotannin kuma sun ce an kai wani harin a garin Gombi da ke jihar.

Sai dai kuma ya zuwa yanzu ba a san adadin mutanen da harin na Yola ya rutsa da su ba.

Wakilin BBC ya ce lokacin da ya kewaya garin da misalin karfe tara na dare ba kowa a kan tituna, saboda mutane sun gudu sun buya.

Wani bawan Allah ya shaidawa BBC cewa ya ga gawar mutum guda da kuma wata mata wadda ke dauke da raunukan da ke nuna alamun harbinta aka yi a asibitin kwararru na Yola, yayin da wani ma’aikacin jinya ya ce akalla mutane goma ne suka rasa rayukansu.

Har yanzu hukumomi ba su yi karin bayani a kan faruwar al’amarin ba.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Mazauna garin Mubi sun shaidawa BBC cewa wadanda suka rasa rayukansu a harin da aka kai da rana a garin na Mubi ’yan kabilar Ibo ne wadanda suka fito daga kudancin Najeriya.

Wadansu rahotannin kuma daga wani sashen yankin na arewa maso gabashin Najeriya ya ce ’yan sanda sun yi musayar wuta da wadansu ’yan bindiga wadanda ake zaton ’yan kungiyar Boko Haram ne a garin Potiskum da ke Jihar Yobe.

A ’yan kwanakin nan dai kungiyar ta kaddamar da hare-hare da dama a yankunan tsakiya da arewacin kasar—ta kuma dauki alhakin kai hari a wata majami’a a garin Madalla wanda ke kusa da babban birnin kasar, Abuja, inda mutane da dama suka rasa rayukansu.

Daya daga cikin bangarorin kungiyar ya gargadi ’yan asalin kudancin kasar—wadanda akasarinsu Kiristoci ne ko mabiya addinan gargajiya—da su bar yankin arewacin kasar, inda Musulmi ke da rinjaye.

Akalla mutane shida aka bayar da rahoton an harbe a wata majami’a a Gombe, a dai yankin na arewa maso gabashin Najeriya.

’Yan kabilar Ibo mazauna garin Mubin da aka kashe suna taro ne don tattauna yadda za a yi a kai gawar wani dan uwansu, wanda wadansu ’yan bindiga a kan babur suka harbe ranar Alhamis da yamma, gida don yi masa jana’iza.

Jihar Adamawa dai na da iyaka da Jihar Borno, inda tushen kungiyar Boko Haram yake.

A watan da ya gabata, shugaban kasa ya kafa dokar ta-baci a jihohin Yobe da Borno a arewa maso gabas, da Filato a tsakiyar kasar, da kuma

Neja a arewa maso yamma, sakamakon karuwar tashe-tashsn hankula masu nasaba da addini da kuma kabilanci.

Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Adamawa, Ade Shinaba, ya shaidawa kamfanin dillancin labari na AP cewa ya yi amanna ’yan kungiyar Boko Haram ne suka kai hare-haren na Mubi.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan kuma, Atine Daniel, ta shaidawa BBC cewa jami’ai sun nufi garin don gudanar da bincike.

Akasarin al’ummar Ibo da ke arewacin Najeriya dai suna da shaguna da wuraren kasuwanci.

Wakilin BBC a Yola, Abdullahi Tasiu Abubakar, ya ce ’yan kabilar ta Ibo da dama sun rufe shagunansu a garin na Mubi suna kuma shirin neman sa’a ga zakara.

Ya kuma kara da cewa yanzu mutane a yankin, daga baki har ’yan gari, na cikin zullumi da zaman dardar.