Ba za mu fasa yajin-aiki ba- 'Yan kwadago

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu zanga-zanga don bijirewa matakin gwamnati na cire tallafin man fetur a Najeriya

A Najeriya, kungiyar kwadago ta NLC ta ce tana kan bakanta na shiga yajin aikin gama-gari wanda ta shirya farawa daga ranar Litinin mai zuwa duk kuwa da umurnin da wata kotun warware rikici tsakanin ma'aikata da masana'antu ta bayar cewa kada kungiyoyin kwadagon su gudanar da yajin aikin.

Umarnin kotun dai ya baiwa hukumomi damar tarwatsa masu zanga-zangar da 'yan kwadagon za su yi, idan suka ci gaba da yajin aikin.

Sai dai Comrade Nuhu Abbayo Toro, mataimakin sakataren kungiyar ta NLC mai kula da shirye-shirye ya shaidawa BBC cewa babu wani umurni da suka samu daga kotun, don haka za su shiga yajin aiki kamar yadda suka tsara.

Kungiyar kwadagon dai ta ce za ta gudanar da yajin-aiki da zanga-zanga ne don bijirewa matakin da Gwamnatin Tarayyar kasar ta dauka na janye tallafin man fetur.

Kungiyoyi da ma 'yan kasar da dama ne suke ci gaba da zanga-zanga don bijirewa matakin gwamnatin, wanda suka ce zai kara jefa su cikin matsanancin hali.

Ita dai gwamnatin ta ce ta cire tallafin ne ganin cewa akasarin 'yan kasar basa amfana daga gare shi.