Ana bikin cikar ANC shekaru dari

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tambarin bikin cika shekaru dari da kafa ANC

Shugabannin siyasa daga sassa da dama na duniya sun hallara a Afirka ta Kudu domin bukukuwan cikar jam'iyyar ANC shekaru dari da kafuwa.

A yanzu haka kuma suna gabatar da addu'o'i a wata majami'ar darikar Methodist a garin Bloemfontein inda aka yanke cibin ANC din a shekarar 1912 don ta yaki mulkin farar fata tsiraru.

Daga bisani kuma shugaban jam'iyyar ta ANC, Shugaba Jacob Zuma, zai jagoranci wani gangamin tunawa da ranar.

Sai dai kuma Nelson Mandela, wanda ya jagoranci hawan jam'iyyar karagar mulki bayan kawo karhsen wariyar launin fata, ba zai halalci bukukuwan ba.