Amurka ta soki gwamnatin Bahrain

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Amurka, Barack Obama

Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta shiadawa Bahrain cewa ta damu matuka da yadda ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula a kasar tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zangar kin jinin gwamnati.

Ma'aikatar Harkokin Wajen ta Amurka ta kuma bukaci gwamnatin Bahrain ta binciki zargin cin zarafin wani fitaccen mai fafautukar kare hakkin bil Adama, Nabeel Rajab.

Mai fafutukar ya ce 'yan sanda sun lakada masa duka yayin wani gangami ranar Juma'a.

Gwamnatin dai ta musanta hakan tana cewa 'yan sandan sun tsinci Mista Rajab ne a kwance jina-jina suka kuma dauke shi zuwa asibiti.

Ba kasafai Amurka ke suka Bahrain ba

Amurka ta ce duk da yake ba a hakikance gaskiyar lamarin ba, amma dai batun na tayar da hankali, musamman yadda rahotannni ke cewa 'yan sandan Bahrain na yin amfani da karfin da ya wuce kima a kan 'yan adawa.

Ba kasafai Amurka ke fitowa fili ta soki gwamnatin Bahrain ba, duk da sukar da kasashen duniya ke yi a kanta, game da musgunawa masu zanga-zangar kin jinin-ta a 'yan watannin da suka gabata.

Amurka na son goyon bayan 'yan rajin tabbatar da mulkin dimokaradiyya a Gabas ta Tsakiya, amma tana matukar goyon bayan gwamnatin Bahrain, wacce 'yan Sunni ke jagoranta.

Kazalika tana da sansanin sojin ruwanta a masarautar ta yankin Gulf.

Kwanakin baya ne dai Sarkin Bahrain ya amince ya gudanar da wadansu sauye-sauye bayan wani rahoto ya nuna cewa ana musgunawa mutanen da ake tsare da su a gidajen yarin kasar.

Karin bayani