Anwar Ibrahim ya samu kubuta

Anwar Ibrahim
Image caption Anwar Ibrahim

Kotu ta sallami jagoran 'yan adawan Malaysia a bisa zargin luwadi, bayan an yi kusan shekaru biyu ana ta tafka shari'a.

An dai zargi Anwar Ibrahim ne da tarawa da wani mai yi masa hidima.

Amma alkali ya ce kwayoyin hallitar sa da aka yi amfani dasu a masayin hujja a shara'ar ba hujja ce mai kwari ba.

Shidai Anwar Ibrahim ya sha jaddda cewa zargin da aka yi masa bashida tushe balle makama.

Wakiliyar BBC tace iyalan sa sun yi ta shewa harda kukan murna lokacin da aka karanto hukuncin.

Da dama daga cikin magoya bayansa sun yi zaman kunci don suna ganin ai tun farko ma bai kamata a gurafanar da shi ba.

Wanna dai shi ne karo na biyu da ake zargin sa da luwadi.

Karin bayani